Sun. May 19th, 2024
(Last Updated On: )

WATA SABUWA: Adam A. Zango ya girgiza Kannywood
 
Jarumi Adam A. Zango ya fallasa dalilansa na yawan sakin auren da yake yi.
 
A sakon da ya wallafa a sahihan shafukansa na Instagram da Facebook ya zargi tsofaffin matansa da aikata manyan laifuka.
 
Tun kafin ya fitar da wanann sako dai Zango ya yi gargaɗi a shafinsa na TikTok cewa kar wanda ya kuskura ya soma cewa da shi ba girmansa ba ne don ya yi tonon silili.
 
A baya-bayan nan dai Zango ya shiga cece kuce a Social Media tun bayan rasuwar Jaruma Daso har ma suka yi musayar kalamai da Dan TikTok ɗin nan da ake kira Dr. Hussaini Kano wanda ya ke zaune a kasar Libiya.
 
Dama tun a can baya Zango ya sha yin barazanar yin tonon silili yana mai cewa mutane ba su san fa hakurin da yake yi ba.
 
Tuni dai wannan tonon silili mafi girma da Zangon ya yi ya zama babban abin tattaunawa a kafafen sada zumunta.
Jarumin ya kira sunan matan nasa har guda hudu,wanda yace zai fadi abinda ya raba su da kowacce su domin ya wanke kansa daga zargin jama’a akan sa.
Sai dai wallafar sa keda wuya,ya faɗi lefukan da aka mishi amman bece ga wacce tayi a cikin su ba, kamar yadda zaku gani a screenshot dake kasa.
Amman daga baya ya goge rubutun da duka bidiyon da yayi bayan jin kiraye kiraye daga mutane da dama
Har kawo lokacin da muke haɗa wannan rahoto babu ɗaya daga cikin tsoffin matan nasa da suka yi martani a kai.
 
Yanzu haka dai Jarumi Adam Zango yana can ƙasar Ghana inda ya ke gabatar da wasan Sallah, kuma rahotonni ya ce ya samu gagarumar tarba a can.
The post Wannan sune dalilan da yasa Adam Zango ya saki matan sa,tonon silili a karon farko ba rufa-rufa appeared first on Labarai.

How useful was this post?

Click on a star to rate it!

Average rating 0 / 5. Vote count: 0

No votes so far! Be the first to rate this post.

As you found this post useful...

Follow us on social media!

We are sorry that this post was not useful for you!

Let us improve this post!

Tell us how we can improve this post?