243 total views, 3 views today
ƳAN MATA DA SAMARI KOWA YAYIWA KANSA
HISABI
• Shin idan ka samu matar aure mai irin halinka sak zaka aureta?
• Shin idan kika sami mijin aure mai irin halinki sak, zaki aureshi?
• Duk wanda yakeson mace tagari, to shima yazama nagari.
• Duk wacce takeson miji nagari, to itama tazama ta gari.
• Bazaka gama zagaye ‘ƴa’ƴan mutane ba, kuma kace bazaka auri wacce aka zagaye ba.
• Bazaki gama sayarda budurcin kiba ga samari ba, kuma kice kinason miji nagari ba.
• Duk irin ɗabi’un da kake kai, kaima irin matar da zaka aura kenan.
• Duk irin ɗabi’un da kike kai, kema irin mijin da zaki aura kenan.
• Dan ALLAH samari da ‘ƴan mata mu gyara halayenmu.
• Duk wanda ya canja halayensa ya kuma tuba to ALLAH zai gafarta masa ya kuma baka abokiyar zama ta gari.
• Duk wacce ta canja ta gyara halayenta kuma ta tuba ALLAH zai gafarta mata ya kuma bata miji nagari.
ALLAH ka azurtamu da abokan zama nagari.
ALLAH kabamu ikon aiki da abinda muka karanta.
ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗaya.
Ameen.
The post Innalillahi!! Duk Wani Matashi Ya Kamata Ya Kalli Wanan Video appeared first on Hausa Blog.